Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan Boko Haram sun kashe manoma 3 tare da sace wasu mata 6 a Nijeriya
2019-11-05 09:25:28        cri

Akalla manoma 3 aka kashe, yayin wani harin da kungiyar Boko Haram ta kai kauyen Rann na jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata majiya ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, mayakan kungiyar sun kuma sace mata 6 yayin harin da ya shafe wasu 'yan sa'o'i a kauyen na Rann, dake yankin karamar hukumar Kalabalge na jihar, a ranar Lahadin da ta gabata.

Mayakan sun farwa manoman ne a lokacin da suke aiki a gona, a kauyen dake kusa da iyakar kasar da Kamaru.

Majiyar ta kara da cewa, yayin da suka harbe maza, mayakan sun yi awon gaba da mata.

Wani ganau, Umar Gamaye, wanda ya tsere a lokacin aukuwar harin, ya ce mayakan sun kai harin ne a kan babura.

Umar Gamaye ya ce, an gano gawarwakin 'yan uwansa manoma ne yayin da 'yan garin ke bincike. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China