Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO:Yaki da cutar zazzabin cizon sauro yana tafiyar hawainiya
2019-12-05 10:04:03        cri
Hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta bayyana cewa, duk da nasarar da aka cimma a duniya a yakin da ake yi da cutar zazzabin cizon sauro, ko malariya a takaice, cikin shekaru goma da suka gabata, ci gaban ya dan ragu a 'yan shekarun nan, kuma hakan na iya mayar da hannun agogo baya.

Hukumar ta bayyana haka ne, cikin wani rahoto game da cutar malariya ta duniya na shekarar 2019 da ta fitar a jiya Laraba.

Rahoton hukumar ya nuna cewa, daga shekarar 2000-2015, an samu raguwar cutar a sassan duniya, inda aka yi kusan nasarar kawar da cutar a kasashe da dama dake fama da ita. Ko da yake a cewar rahoton, a 'yan shekarun nan, ci gaban da aka samu wajen rage sabbin masu fama da cutar a duniya ya ragu.

Bugu da kari, yawan wadanda ke mutuwa sanadiyar cutar a duniya shi ne ya ragu, yayin da adadin wadanda suka mutu sanadiyar cutar a shekarar 2016-2018 ya yi kasa bisa na shekarar 2010-2015, kana yara 'yan kasa da shekaru biyar sun kai kaso 2 bisa uku ko kaso 67 cikin 100 ne na wadanda suka mutu sanadiyar cutar a duniya a shekarar 2018.

Rahoton ya kara da cewa, matsalar cutar ta fi Kamari a Afirka, Inda a shekarar 2018, ofishin hukumar WHO dake shiyyar Afirka, ya bayyana cewa, matsalar dake da nasaba da cutar a duniya ta kai kaso 93 cikin 100, yayin da sama da rabin dukkan matsalar cutar, tana kasashe 6 na Afirka , wato, Najeriya da Jamhuriyar demokiradiyar Congo, Uganda da Cote d'Ivoire da Mozambique da Jamhuriyar Nijar .(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China