Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
FAO ta lashi takobin tallafawa amfani da sinadaran kashe kwayoyin hallitu a nahiyar Afrika
2019-11-19 10:43:47        cri
Hukumar samar da abinci da kula da harkokin noma ta duniya (FAO), ta yi alkawarin tallafawa amfani da sinadaran kashe kwayoyin hallitu yadda ya kamata a tsarin aikin gona na Afrika.

Babban jami'in kula da lafiyar dabbobi da kiwon dabbobin gida na ofishin hukumar a Afrika, Scott Newman, ya ce tallafin zai taimaka wajen rage rashin tasirin sinadaran a tsarukan aikin gona da muhalli.

Scott Newman ya bukaci samar da mabanbantan dabaru da suka kunshi bangarorin kiwon lafiyar al'umma da dabbobi, da na aikin gona da bangaren muhallin halittu da tsirrai, domin magance rashin tasirin sinadaran.

La'akari da hadduran dake tattare da sinadaran kashe kwayoyin hallitu, hukumomin FAO da WHO da shirin kula da muhalli na MDD ne suka samar da wani shiri kan amfani da sinadaran a kasashen Afrika 10, da suka hada da Kenya da Burkina Faso da Senegal da Zimbabwe domin tallafawa shirin kasashen duniya na magance rashin tasirin sinadaran. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China