Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin CDB na Sin zai ba da rancen kudi don aikin gina tashar tekun Lekki a Najeriya
2019-10-25 15:12:53        cri

A ranar 23 ga wata, a birnin Lagos, babban birnin kasuwancin Najeriya, aka shirya bikin daddale yarjejeniyar samar da rancen kudi dala miliyan 629 da bankin raya kasar Sin na CDB ya bayar, don aikin gina tashar tekun Lekki na Najeriya. Lamarin da ya shaida cewa, za a fara aikin gina tashar a hukumance tun da an riga an samu kudi.

Aikin gina tashar tekun Lekki yana yankin cinikayya marasa shinge na Lekki, wanda yake bakin mashigin Guinea na tekun Atlantika, kilomita 60 daga gabashin birnin Lagos. Bisa shirin da aka tsara, za a gina manyan wurare biyu na daure jirgin ruwa a turke a matakin farko, wadanda za su iya daure jiragen ruwa masu dakon kwantenoni 18000, kuma yawan kwantenonin da za a dora da saukewa, zai kai miliyan 1.2 a duk shekara. Yawan kudin da za a kebe a cikin wannan aikin ya kai dala biliyan 1 da miliyan 43, kana kamfanin Harbour Engineering na kasar Sin (CHEC) da kamfanin Tolaram na kasar Singapore, da hukumar kula da ayyukan tashoshin teku ta Najeriya, da ma gwamnatin jihar Lagos ne za su hada hannu tare wajen gudanar da aikin.

Lin Yichong, babban daraktan kamfanin CHEC ya bayyana cewa, daddale yarjejeniyar samar da kudi ga aikin gina tashar tekun Lekki ya alamta cewa, an riga an samu dukkan sharudan gudanar da aikin, don haka za a iya fara aikin ginin a hukumance. Lin ya kara da cewa,

"Aikin gina tashar tekun Lekki wani muhimmi aiki ne da za a kaddamar a karkashin laimar tsarin FOCAC da shawarar 'ziri daya da hanya daya', wanda zai taka muhimmiyar rawa wajen kyautata ayyukan more rayuwa na tashoshin tekun Najeriya, da yanayin zirga-zirga da ma bangaren zuba jari na kasar, baya ga sa kaimi ga aikin samar da guraben aikin yi ga mazauna wurin. An yi imanin cewa, aikin zai yi babban tasiri wajen ci gaban tattalin arzikin jihar Lagos har ma na duk fadin Najeriya."

A nasa bangaren, Biodun Dabiri, shugaban hukumar daraktoci na tashar ruwan Lekki yana ganin cewa, daddale yarjejeniyar samar da rancen kudi ga aikin na da babbar ma'ana, sa'an nan aikin gina tashar tekun Lekki zai ba da babbar gudummawa ga bunkasar yankin cinikayya marasa shinge na Lekki. Yana mai cewa,

"Samar da rancen kudi dala miliyan 629 da bankin CDB ya yi ya zama tamkar wata ishara. Ban da wannan kuma, kamfanin CHEC na Sin ya zuba jarin dala miliyan 230 kai tsaye ta hanyar samun ikon mallakar hannayen jari. Duk lamuran biyu za su tabbatar da kammala aikin gina tashar ruwan Lekki na matakin farko yadda ya kamata, baya ga tabbatar da cewa, Najeriya za ta kasance babbar cibiyar harkokin fito ta ruwa a yankin kudu da hamadar Saharar Afrika."

Bisa shirin bankin CDB, reshensa da ke birnin Dalian zai kula da aikin samar da rancen kudin cikin dogon lokaci, domin goyon bayan aikin ginawa da tafiyar da harkokin tashar. Zhang Aijun, mataimakin shugaban reshen CDB da ke birnin Dalian ya furta a gun bikin daddale yarjejeniyar cewar:

"Daddale yarjejeniyar ya kasance matakin farko ne kawai, ana fatan kamfanin kula da aikin zai kara mai da hankali kan gudanar da aikin, da kara kwarewar tinkarar hadari, da ma tafiyar da yarjeniyoyi cikin tsanaki, a kokarin tabbatar da kammala aikin ginin yadda ya kamata. Mun yi imanin cewa, bisa kokarin bangarori daban daban, da ma goyon bayan da gwamnatin Najeriya ke nunawa, za mu cimma burinmu cikin nasara. A waje daya kuma, bankin CDB na fatan yin amfani da wannan damar wajen ci gaba da raya ayyukansa a Najeriya, a kokarin ba da gudummawa ga bunkasar tattalin arzikin kasar."

An labarta cewa, an kaddamar da aikin gina tashar ruwan Lekki a ranar 1 ga watan Satumba, wanda zai kwashe watanni 30 ana yinsa. Bayan kammalar aikin kuwa, tashar ruwan Lekki za ta kasance daya daga cikin tashoshin ruwa mafiya zurfi a cikin teku a yammacin Afirka, wanda zai kara karfin dorawa da sauke kwantenoni na tashoshin ruwa da ke yammacin Najeriya, da sassauta matsalar cunkoson tafiye-tafiye na birni da yankin tashar teku, da ma rage yawan kudin da ake kashewa wajen jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China