Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi tir da dokar hakkin Bil Adama da dimokuradiyya kan Hong Kong da Amurka ta zartas
2019-11-28 19:03:24        cri
Ofishin kula da harkokin Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba da wata sanarwa a yau Alhamis, inda da kakkausar murya ya yi tir da dokar hakkin Bil Adama da dimokuradiyya kan Hong Kong da Amurka ta zartas.

A jiya ne, Amurka ta zartas da wannan doka, wadda kasar Sin ta yi biris da matukar nuna rashin jin dadinta, domin wannan mataki tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma ya keta dokar kasa da kasa da ka'idojin dangantakar kasa da kasa.

Dadin dadawa, sanarwa ta nuna cewa, gwamnatin kasar Sin za ta tsaya tsayin daka don kiyaye 'yanci da tsaron kasa da ma muradun bunkasuwarta, kana za ta nace ga manufar "kasa daya tsarin mulkin biyu ", tana kuma adawa da duk wani yunkuri na yin shisshigi a harkokin yankin Hong Kong. Yunkurin Amurka na hana bunkasuwar kasar Sin ta hanyar tada tsaune tsaye a Hong Kong ba zai yi nasara ba ko kadan, kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China