Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi tir da hari kan motar jami'an MDD a Kabul
2019-11-25 14:17:01        cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin da aka kaiwa wata mota, mai dauke da jami'an MDD a birnin Kabul na Afghanistan, lamarin da ya hallaka jami'i daya, tare da jikkata wasu mutane biyu.

Cikin wata sanarwa da kakakin sa Stephane Dujarric ya fitar, Mr. Guterres ya bayyana matukar alhini, tare da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, yana mai fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin Afghanistan, da ta yi duk mai yiwuwa, wajen tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata wannan ta'asa, yana mai ba da tabbacin cewa, MDD za ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al'ummar Afghanistan, a yunkurin su na tabbatar da zaman lafiya, da ci gaba mai dorewa a kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China