Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe dalibi guda a yanki mai magana da Turanci a Kamaru
2019-11-11 09:37:29        cri

Yan bindiga sun kashe wani dalibin jami'ar Bamenda a yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru da ake magana da yaren Turanci, inda ake fama da rikici, kana an yi garkuwa da wasu dalibai 8 a ranar Lahadi, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.

Hukumar 'yan sandan yankin ta ce, an harbe dalibin ne har lahira a lokacin da ya dage kai da fata cewa ba zai amincewa masu garkuwar su yi awon gaba da shi ba.

Hukumar gudanarwar jami'ar ta yi Allah wadai da kisan dalibin sannan ta bukaci a gaggauta sako daliban 8 da masu garkuwar suka kwashe.

Yan sanda sun zargi mayakan 'yan aware da laifin yin garkuwar, zargin da 'yan awaren suka musanta.

Su dai mayakan 'yan awaren sun sha alwashin dakatar da dukkan makarantun dake yankunan masu magana da yaren Turanci a kasar, matukar aka gaza daukar matakan neman tattaunawar sulhu da tsakaita bude wuta don kawo karshen rikicin dake addabar yankunan.

Jamhuriyar Kamaru wadda galibi suke magana da yaren Faransanci sun jima suna fuskantar hare haren mayakan 'yan aware masu magana da yaren Turanci dake shiyyoyin arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar, inda 'yan awaren ke fafutukar neman ballewa don kafa kasa mai cin gashin kanta.

A cewar MDD, tashin hankalin wanda ya fara a shekarar 2017, ya yi sanadiyyar raba mutane sama da 530,000 daga gidajensu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China