Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: Hauhawar farashin kayayyaki ya karu zuwa kaso 11.61 bisa dari
2019-11-18 20:41:53        cri

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar da wani rahoto dake cewa, ya zuwa watan Oktoba da ya gabata, hauhawar farashin kayayyakin masarufi ya karu zuwa kaso 11.61 bisa dari.

Hukumar ta NBS ta kara da cewa, alkaluman gwajin hauhawar kayayyaki na CPI sun karu a watan na goma, idan aka kwatanta da na watan Satumba, lokacin da aka samu kaso 11.24 bisa dari.

Kaza lika hukumar kididdigar ta ce, bisa alkaluma na wata wata, alkaluman na CPI sun karu da kaso 1.07 a watan Oktoba, karin kaso 0.03 bisa dari ke nan, sama da kaso 1.04 bisa dari da aka samu a watan Satumba.

Rahoton ya bayyana cewa, karuwar farashin abinci ya auku ne sakamakon karuwar farashin nama, da mai da kitse, da biredi da hatsi. Sai kuma dankali, da doya da dangogin ta, da kifi da kuma ganyaye.

Masana a Najeriyar dai na ganin wannan karuwar farashin kayayyaki, na da nasaba da rufe kan iyakokin kasar da mahukuntan Najeriyar suka aiwatar, wanda ya sabbaba katsewar harkokin shige da ficen kayayyaki ta kan iyakokin kasar ta kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China