Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamian Sin da Amurka sun tattauna ta wayar tarho kan ciniki
2019-11-17 15:08:56        cri

Mataimakin firaministan kasar Sin, mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS, kana babban jami'in bangaren kasar Sin game da tattauna batun warware takaddamar cinikin Sin da Amurka Liu He, ya yi tattaunawa ta wayar tarho bisa bukatar da wakilin kasuwancin kasar Amurka Robert Lighthizer da sakataren baitil malin Amurka Steven Mnuchin suka nema da safiyar ranar Asabar.

A lokacin tattaunawar tasu, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai matukar muhimmanci game da babbar moriyar dake shafar bangarorin biyu na zagayen farko da aka cimma matsaya kansu, kana sun amince za su ci gaba da tuntubar juna akai-akai kan batun.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China