Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Nijeriya sun fatattaki 'yan ta'addan Boko Haram a Borno
2019-11-17 16:26:23        cri

Bisa labarin da muka samu daga shafin intanet na jaridar Leadership ta Najeriya a yau, an ce, sojojin Nijeriyar sun sake samun gagarumar nasarar wajen fatattakan mayakan 'yan ta'addan Boko Haram da mayakan dake neman kafa daular musulunci a yammacin Afrika, (ISWAP), a garin Malam Fatori, na karamar hukumar Abadam, ta jihar Borno.

Shugaban sashen yada labarai na rundunar sojojin Kanar Aminu Iliyasu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Iliyasu ya ce 'yan ta'addan sun yi yunkurin kaddamar da wani hari ne a wajen da dakarun tsaro na runduna ta 64 da ta 98 suke a ranar Juma'a.

Ya ce 'yan ta'addan sun yi yunkurin daukar fansa ne kan fatattakar da jami'an sojojin suka yi musu a kokarin da suka yi na kutsawa wajen jami'an rundunar wanda bai yi nasara ba.

A hare hare biyu da dakarun sojojin suka kai sun yi nasarar lalata babbar motar yakin mayakan tare da kashe 'yan ta'adda uku dake cikinta.

Iliyasu ya kara da cewa, an kuma sake kashe wasu 'yan ta'addan guda biyu a lokacin bata-kashin, kana an kuma kwato kayan yaki masu yawa, da suka hada da bindigar kakkabo jiragen sama, da AK-47 guda takwas da kuma bindigar harba roka guda daya, da kwanson harsashin AK-47 guda uku da sauransu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China