Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin:Ci gaba mai dorewa shi ne ginshikin sasantawa
2019-11-20 11:05:30        cri
Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana ci gaba mai dorewa a matsayin muhimmiyar dabara ta sasantawa da ma magance duk wasu abubuwan dake haddasa tashin hankali daga tushe.

Zhang jun, ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD cewa, galibin manyan rikice-rikice na kasa da kasa da shiyya-shiyya, sun samo asali ne sakamakon talauci da rashin ci gaba.

A don haka ya ce, wajibi ne a mayar da hankali kan batun zaman lafiya da ci gaba, da tabbatar da zaman lafiya da hanyar ci gaba, daidaita bunkasuwa ta hanyar zaman lafiya, magance dukkan alamomi da ma dalilan da ke haddasa tashin hankali daga tushe, da aza harsashin sasantawa da zaman lafiya mai karfi ta hanyar kara karfin dabarun ci gaba.

Bugu da kari, jami'in na kasar Sin, ya tabo rawar da " ofisoshi masu kyau da shiga tsakani" za su taka wajen cimma nasarar sasantawa.

A dangane da wannan batu, Zhang ya ce wajibi ne hukumar kwamitin sulhu ta dauki matakan da suka dace, kana kungiyoyi na shiyya-shiyya da ma rassansu, su ma su sauke nauyin dake bisa wuyansu yadda ya kamata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China