Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Muhallin gudanar da harkokin kasuwanci a kasar Sin ya samu kyautatuwa
2019-10-24 13:40:07        cri

Bankin duniya ya gabatar da wani rahoto dangane da muhallin gudanar da harkokin kasuwanci a kasashe daban daban a yau Alhamis, wanda ya nuna cewa matsayin kasar Sin cikin kasashen duniya a fannin samar da ingantaccen muhallin kasuwanci ya karu zuwa na 31, kana kasar tana cikin jerin kasashe 10 wadanda suka fi samun ci gaba a kokarin kyautata muhallin gudanar da harkokin kasuwanci cikin shekaru 2 a jere.

Martin Raise, shi ne darekta mai kula da batun da ya shafi kasar Sin na bankin duniya. Ya ce, kasar Sin ta dukufa wajen kyautata muhallin kasuwanci don amfanawa kanana da matsakaitan kamfanonin kasar, tare da daukar matakan gyare-gyare masu kyau, saboda haka, kasar ta samu ci gaba mai gamsarwa a fannin samar da muhallin kasuwanci mai inganci.

Tun daga shekarar 2003, bankin duniya ya fara gabatar da rahoton muhallin kasuwanci na kasashen duniya a kowace shekara, inda ya kan ba da maki ga kasashe 190, gami da sanya su cikin wani jeri na ingancin muhallin kasuwanci. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China