Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta jaddada bukatar tabbatar da kasashe biyu a matsayin hanyar warware batun Falasdinu
2019-10-29 13:23:41        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce ya kamata a tabbatar da burin kafa kasashe biyu wajen warware batun Falasdinu.

Da yake jawabi ga kwamitin sulhu na MDD, Zhang Jun, ya ce manufar kafa kasashe biyu da kuma janyewar Isra'ila daga yankunan Falasdinu, su ne za su tabbatar da adalcin duniya, wanda kuma ba zai yiwu a kara janyewa daga gareshi ba.

Zhang Jun, ya jaddada cewa, kafa kasa 'yantacciyar kasa, cikakken 'yanci ne na al'ummar Falasdinu, kuma ya kamata kasashen duniya su mara baya ga batun kafa kasashe 2, da kudrorin MDD masu alaka da batun da manufar janye mamayar Isra'ila, domin tabbatar da zaman lafiya da sauran matsayar da kasashen duniya suka cimma da kuma dawo da tsarin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya bisa turba.

Ya ce babban aikin shi ne, daukar matakin kare ta'azzarar zaman dar-dar da sake dawo da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra'ila nan ba da dadewa ba.

Ya ce a shirye kasar Sin take ta ci gaba da hadin gwiwa da Falasdinu a fannonin tattalin arziki da harkokin kudi da al'adu da ilimi da kiwon lafiya da kuma ci gaba da daukar matakai masu kwari na inganta zaman lafiya da ci gaban Falasdinu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China