![]() |
|
2019-11-02 15:33:43 cri |
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, kuma mamban hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kuma jagoran tawagar Sin a tattaunawar da ake tsakaninta da Amurka kan harkokin cinikayya, ya tattauna ta wayar tarho bisa gayyatar da wakilan bangaren Amurka suka yi masa, wato Robert Lighthizer da sakataren kudin kasar, Steven Mnuchin.
Bangarorin 2 sun tattauana sosai kuma mai ma'ana, kan yadda za su magance batutuwan dake ci musu tuwo a kwarya da kuma cimma matsaya guda.
Bangarorin biyu sun kuma tattauna kan shirye-shiryen tattaunawarsu ta gaba. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China