Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadarin kwale kwale ya yi sanadin mutuwar mutum 1 a Kamaru
2019-11-05 09:37:41        cri

Rundunar sojin ruwan Kamaru, ta ce an ceto sama da mutane 20, yayin da mutum 1 ya mutu, biyo bayan kifewar wani kwale-kwale a kusa da Idenau, garin dake gabar teku a yankin kudu maso yammacin kasar.

Wadanda suka tsiran sun ce masu kamun kifi ne suka fara isa wajensu, inda suka ceci fasinjoji a lokacin da kwale kwalen ya kife.

A cewar rundunar sojin ruwan, daga bisani ne masu ceton daga rundunar suka isa wajen, inda suka hada hannu da masu kamun kifin wajen aikin ceton da rundunar ta bayyana a matsayin wanda ya cimma nasara.

Jami'an sun ce, mutum guda ya mutu a cikin teku yayin da yake kokarin iyo don tsira, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba. Har ila yau, sun ce ana ci gaba da aikin ceton don binciko wadanda mai yiwuwa sun bata.

Fasinjojin da galibinsu dalibai ne da 'yan kasuwa na Kamaru da 'yan Nijeriya, na kan hanyarsu ne ta zuwa garin Idenau, daga garin Mundemba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China