Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 3 sun mutu a hadarin jirgin ruwa a tsakiyar Najeriya
2019-11-06 09:39:45        cri

An gano gawarwakin mutane 3, kana wasu mutane 4 sun bace a sanadiyyar kifewar kwale kwale a kogin tsakiyar Najeriya, wani jami'in yankin ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

Kwale kwalen wanda aka bayyana cewa ya yi lodin da ya wuce kima a lokacin da lamarin ya faru, ya kife ne a tsakiyar kogin Gwayaka dake kusa da Lafia, babban birnin jihar Nasarawa dake shiyyar arewa maso tsakiyar Najeriya, da yammacin ranar Juma'a.

Shuaibu Zanwa, jami'in karamar hukumar lafiya ta gabas, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu mutanen sun tsira da ransu a hadarin.

Zanwa ya ce, ya zuwa ranar Litinin, an gano gawarwakin mutane 3 ne bayan da wasu mutanen yankin tare da hadin gwiwar jami'an tsaro suka gudanar da aikin ceto. Har yanzu ana ci gaba da aikin gano ragowar mutanen da suka salwanta wadanda ruwa ya yi awon gaba da su.

Wata majiya daga yankin ta ce, wani fasinja ne ya yi sanadiyyar hadarin wanda ba'a tabbatar da kwarewar sarrafa kwale kwalen ba.

A cewar jami'in dan sandan yankin, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin dalilin da ya haddasa kifewar kwale kwalen.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China