Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sake bukatar Amurka da ta daina gurgunta wasu kamfanoninta
2019-10-29 18:58:25        cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da matakan Amurka na gurgunta wasu kamfanoninta ba gaira ba dalili, kuma ta sake bukatar ta da ta daina yin haka.

Rahotanni na cewa, kwanan baya kwamitin sadarwar tarayyar Amurka wato FCC a takaice ya bayar da wata sanarwa cewa, zai jefa kuri'a kan wani kudurin dake shafar kamfanonin Huawei da ZTE na kasar Sin, inda za a hana 'yan kasuwan dake sayar da na'urorin sadarwa na Amurka su sayi na'urorin da wadannan kamfanonin biyu suke samarwa ta hanyar yin amfani da asusun FCC, saboda wai na'urorin kamfanonin kasar Sin za su kawo hadari ga tsaron kasar ta Amurka.

Kan wannan, Geng Shuang ya bayyana cewa, matakin nuna fin karfin da Amurka ta dauka ya sabawa ka'idar tsarin kasuwar da take bayyanawa, don haka, zai yi wahala ya samu goyon bayan al'ummomin kasashen duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China