Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jarin kai tsaye dake shiga Sin ya karu da kaso 6.6 bisa dari cikin watanni 10
2019-11-18 19:11:55        cri

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ko MOC a takaice, ta ce yawan jarin kai tsaye da ake zubawa a babban yankin kasar Sin, ya karu da kaso 6.6 bisa dari, tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban shekarar nan da muke ciki, inda darajar sa ta kai kudin Sin Yuan biliyan 752.41. Kaza lika a tsakanin watannin 10, an kafa sabbin kamfanoni masu jarin waje, wadanda yawan su ya kai 33,407.

Alkaluman da hukumar ta fitar sun kuma nuna cewa, darajar jarin waje a fannin masana'antun manyan fasahohin zamani ta karu, da kusan kaso 39.5 a tsakanin shekara daya, inda darajar kudin da aka shigar fannin ta kai Yuan biliyan 222.4, wato kimanin kaso kusan 30 bisa dari ke nan na jimillar jarin na waje dake shigowa Sin.

Bugu da kari, wannan adadi wanda ya shafi yankin zirin tattalin arziki na kogin Yangtze, ya daga da kaso 8 bisa dari, zuwa Yuan biliyan 368.3, wato kaso 49 bisa dari ke nan na jimillar jarin waje da kasar ke samu. Har ila yau, yawan jarin waje dake shigowa fannin yankin cinikayya maras shinge na gwaji da Sin din ke aiwatarwa, ya karu da kaso 23.9 bisa dari, wato kimanin Yuan biliyan 108.4 ke nan cikin shekara daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China