Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kudi da za a kashe karkashin fasahar "blockchain" a Sin nan da 2023 zai haura dala biliyan 2
2019-11-11 10:39:45        cri
Wani rahoto da kamfanin IDC mai bincike game da hada hadar cinikayya ta na'urorin zamani ya fitar, ya nuna cewa, yawan kudi da za a kashe, karkashin fasahar killace bayanai ta na'urorin zamani ko "blockchain" a takaice a nan Sin, nan da shekarar 2023 zai haura dala biliyan 2.

Rahoton ya ce bisa kiyasi, yawan kudaden da za a kashe a kasar ta Sin kan raya wannan fanni, za su karu da kaso kusan 65.7 bisa dari a duk shekara tsakanin shekarar 2018 zuwa 2023.

A shekarar nan ta 2019, mafi yawan kudaden da aka kashe a fannin cin gajiyar wannan fasaha, sun shafi fannin bankuna ne, sai kuma fannonin sarrafa kayayyaki, da na sayar da hajoji, da ayyukan ba da hidima da na ayyukan masana'antu.

Fasahar "blockchain" dai na baiwa sassan masu amfani da ita damar tattara bayanai, da sarrafa amfani da su ta yanar gizo cikin wani yanayi mai karfin kariya daga kutse. Kaza lika ana amfani da wannan fasaha wajen musayar kudade ta yanar gizo, maimakon amfani da bankuna da aka saba da su bisa al'ada.

Yayin wani zama na nazari game da wannan fasaha, wanda ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya gudanar a watan jiya, jagororin kasar ta Sin sun jaddada muhimmancin fadada kirkire kirkire, da sauye sauye a fannin masana'antu ta hanyar raya wannan fasaha. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China