Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana maraba da kamfanonin ketare su zuba jari a cikin kasar
2019-10-10 20:04:34        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa tana maraba da kamfanonin ketare, ciki har da na Amurka, da su zuba jari su kuma gudanar da harkokinsu a cikin kasar.

Mr Geng ya bayyana hakan ne, a taron manema labarai, lokacin da yake mayar da martani kan zargin da wasu jami'an Amurka, da masu tsara dokoki da kafofin watsa labarai suka yi cewa, kasar Sin tana danne kamfanonin Amurka har ma tana tilasta musu watsi da muradunsu.

Ya ce, a 'yan shekarun baya-bayan nan, kasar Sin ta ci gaba da inganta yanayin kasuwanci ga baki masu sha'awar zuba jari, kuma kasar Sin ta dade da zama daya daga cikin wurare masu yanayin zuba jari mai kyau da kamfanoni daga sassan duniya ke sha'awar zuwa.

Ya ce, wani rahoton bincike na baya-bayan, ya nuna cewa, kaso 97 cikin 100 na kamfanonin Amurka sun samu riba mai tarin yawa a kasar Sin, kana kaso 74 cikin 100 na mambobin majalisar 'yan kasuwan Amurka dake kasar Sin, suna shirin kara zuba jari a cikin kasar Sin.

Don haka, idan har Amurkawa sun yarda, za a iya cewa, dukkan wadannan kamfanonin na Amurka, an tilasta musu watsi da muradunsu, kana kasar Sin ta danne su?

Geng ya ce, manufofin kasar Sin na samarwa kamfanonin ketare yanayin da ya dace da ma, manufofinta na kare halattun 'yancin kamfanonin ketare ba za su canja ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China