Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta yi aikin bincike a duniyar Mars a shekarar 2020
2019-11-14 15:26:04        cri
Yau Alhamis, Sin ta yi gwajin na'urar sauka a duniyar Mars a birnin Huailai na lardin Hebei na kasar Sin, wannan shi ne karo na farko da Sin ta bayyana za ta yi aikin bincike a duniyar Mars a fili. Kuma Sin za ta gudanar da aikin bincike a duniyar Mars a shekarar 2020.

A yau kuma, hukumar harkokin zirga-zirga a sararin samaniya ta kasar Sin ta gayyaci mutane kimanin guda 70, wadanda suka hada da jakadun kasashen ketare dake kasar Sin su 19, da wakilan tawagogin jakadun kungiyar EU da na kungiyar AU dake nan kasar Sin, da wakilan kungiyar hadin gwiwar harkokin zirga-zirga a sararin samaniya ta Asiya da Pacific, da kuma 'yan jaridu na kasar Sin da na kasashen ketare, don su halarci taron gwajin.

Wannan taro ya kasance muhimmin matakin da kasar Sin ta dauka wajen habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen duniya, a fannin aikin zirga-zirga a sararin samaniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China