2019-11-13 14:06:44 cri |
A yau Laraba, an kaddamar da taron musayar fasahohin zamani karo na 21 a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin. Karkashin babban jigon taron na " gina yankin mashigin teku na Guangdong-Hongkong-Macau, gami da bude kofa, da kirkiro sabbin fasahohi", mahalarta taron za su nuna gami da musayar wasu sabbin fasahohi da kayayyaki masu alaka da fasahar sadarwa, da tsimin makamashi, da kulawa da birane, da samar da kayayyaki, da dai sauransu.
Wasu tawagogi 68 na ketare, wadanda suka zo daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 44, kamarsu Argentina, da Australia, da Japan, da Amurka, da tarayyar Turai, da dai sauransu, za su halarci taron na wannan karo. (Bello Wang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China