Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe baje kolin CIIE karo na 2 da yarjejeniyar ciniki ta dala biliyan 71.13
2019-11-10 19:52:07        cri
A yau Lahadi aka kammala bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakinn da ake shigo da su kasar Sin (CIIE) karo na 2, inda aka karkare da cimma yarjejeniyoyin cinikyayyar kayayyaki da ayyukan hidima na tsawon shekara guda wanda yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 71.13.

Sun Chenghai, mataimakin daraktan shirya baje kolin CIIE, ya fadawa taron manema labaru cewa, adadin ya karu da kashi 23 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara.

Baki daya kimanin kasashen duniya 181, da shiyyoyi da kuma kungiyoyin kasa da kasa ne suka halarci bikin, inda kamfanoni sama da 3,800 ne suka halarci bikin baje kolin na wannan karo. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China