Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na da baki daga Faransa
2019-11-09 19:44:54        cri
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kan zo kasar Sin cikin ko wace shekara, kana, bayan ziyararsa a biranen Xi'an da Beijing, a bana, ya tafi can birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin.

A rana ta farko, an shirya liyafar maraba da zuwansa a kasar Sin a gidan sauke baki na Heping.

Yayin liyafar, shugabannin kasashen Sin da Faransa sun tattauna kan bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su Sin mai bude kofa ga waje CIIE, a waje daya kuma, za mu iya duba babban canjin kasar Sin, bayan ta fara bude kofa ga waje.

A safiyar rana ta biyu, shugabannin biyu sun halarci bikin bude baje kolin CIIE, a sa'i daya kuma, matan shugabannin biyu sun ziyarci wata makarantar sakandare dake birnin Shanghai.

Sa'an nan, a daren wannan rana, suka dawo birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, domin fara ziyarar aiki a hukumance. A lokacin da suke ban kwana da juna, fitilu a kan cibiyar birnin Shanghai sun canja launukansu zuwa launin ja, da launin fari da kuma launin shudi, domin nuna fatan alheri ga bakin na kasar Faransa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China