Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhun MDD ya yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar Riyadh kan Yemen
2019-11-07 15:05:16        cri

Kwamitin sulhun MDD, ya yi maraba da yadda gwamnatin Yemen da majalisar rikon kwaryar kudancin kasar, suka sanya hannu kan wata yarjejeniya game da kasar ta Yemen a birnin Riyadh na kasar Saudiya.

Wata sanarwa da aka fitar, ta bayyana yadda mambobin kwamitin sulhun suka amince cewa, yarjejeniyar wani ci gaba ne, kuma muhimmin mataki a kokarin da ake na kawo karshen rikicin siyasar kasar Yemen.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China