Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin jakadancin Sin na tuntubar 'yan sandan Birtaniya game da rahoton gawarwakin da aka gani cikin wata babbar mota
2019-10-25 09:47:46        cri

Ofishin jakadancin kasar Sin a Birtaniya, ya ce yana tuntubar 'yan sandan kasar domin neman tabbaci da sahihancin rahotannin kafafen yada labarai da ke cewa, gawarwaki 39 da aka samu cikin wata babbar mota a yankin Essex, Sinawa ne.

Cikin wata sanarwa, ofishin ya ce ya yi jimamin jin rahoton gawarwakin 39 a Essex na Ingila. Yana mai cewa, ofishin na tuntubar 'yan sandan yankin domin neman tabbaci kan rahotannin.

A daren ranar Alhamis ne, wani kakakin ofishin jakadancin ya ce tuni aka aike da tawaga karkashin jami'n dake kula da harkokin ofishin jakadancin zuwa Essex, kuma sun gana da 'yan sandan yankin.

'Yan sandan sun ce, suna kan tantance asalin mamatan, wadanda kawo yanzu ba za a iya tabbatar da kasarsu na asali ba.

A cewar rahotannin kafafen yada labarai, babbar motar da aka samu gawarwakin cikinta a ranar Laraba da ta gabata a Essex, ta isa Ingila ne bayan ta wuce ta tashar ruwan Zeebrugge, wadda ta kasance tashar jigilar kwantainoni da kayayyaki da fasinjoji a yankin Burges na Belgium.

A cewar kakakin, ofishin jakadancin ya nemi 'yan sandan Belgium da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki su gudanar da cikakken bincike.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China