Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU tace ana samun tafiyar hawainiya wajen tafiyar da harkokin kudaden gwamnati a Afrika
2019-10-14 11:02:44        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar cewa har yanzu cigaban da ake samu ta fuskar tafiyar da harkokin kudaden gwamnati a kasashen Afrika bai taka kara ya karya ba, kasancewar har yanzu kasashen Afrika suna fuskantar koma bayan tafiyar da harkokin kudade.

Kungiyar mai mambonin kasashen Afrika 55, ta lura cewa, gwamnatocin kasashen Afrika da dama da sassan dake tafiyar da al'amurran kudi suna samun gagarumin cigaba wajen cigaba da inganta fannin tafiyar da kudaden, sai dai cigaban bai taka kara ya karya ba kuma wasu da dama daga cikin kasashen na Afrika har yanzu suna dandana kudarsu ta fuskar tafiyar da harkokin kudaden.

AU ta sanar cewa, matsalolin rikicin basukan dake kan kasashe ya sanya ala tilas ake ta kokarin neman hanyoyin tafiyar da harkokin kudade a kungiyoyi da hukumomin kudade na duniya.

Kiran na kungiyar AU ya zo ne kwanaki kadan gabanin gudanar da babban taron koli kan sha'anin kudade na nahiyar Afrika, wanda aka tsara gudanarwa tsakanin 14 zuwa 18 ga watan Oktoba a helkwatar kungiyar tarayyar Afrika dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, taken taron shi ne "Karfafa fannin tafiyar da kudade a Afrika."(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China