Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran za ta kai mataki na uku na kwance shirin nukiliyarta
2019-09-05 11:02:21        cri

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya sanar a jiya Laraba cewa, kasar Iran za ta shiga mataki na uku na kwance shirin nukiliyarta karkashin cikakkiyar yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015, wacce aka fi sani da (JCPOA).

Gidan talabijin na IRIB TV na kasar, ya ambato Rouhani yana cewa, duk da irin nasarorin da aka cimma a yayin tattaunawar da aka gudanar tsakanin Iran da bangarorin kasashen Turai kan batun nukiliyar, har yanzu ba'a kai ga matakin karshe ba.

A don haka Rouhani ya ce, Iran za ta hau mataki na uku na kwance shirinta na nukiliya, kuma nan ba da jimawa za ta sanar da matsayarta kan batun.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China