Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin ya bunkasa kwarewa a Sudan ta kudu
2019-11-06 09:09:57        cri

Darektan reshen kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin mai suna "PowerChina" dake Sudan ta kudu Wang Cun, ya bayyana cewa, 'yan kasar Sudan ta kudu da wasu 'yan asalin kasashen gabashin Afirka dake aiki da kamfanin dake aikin raba wutar lantarki a Juba, sun amfana da kwarewar takwarorinsu Sinawa ma'aikatan kamfanin.

Wang Cun ya bayyana cewa, manufar aikin wanda ake gudana karkashin tallafin bankin raya Afirka tun a shekarar 2016, ita ce farfado da aikin raba wutar lantarki a Juba, wanda tuni ya taimaka matuka wajen farfado da rayuwar daruruwan ma'aikata mazauna wurin

Jami'in ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin wata zantawa a Juba jiya Talata cewa, kamfanin ya dauki sama da ma'aikata 400 mazauna wurin, a matsayin leburori, makanikai da masu aikin lantarki, baya ga masu kula da manyan injuna da ya dauka daga kasashen Uganda da Kenya. Ya zuwa yanzu kamfanin ya dauki sama da ma'aikata 48 daga shiyyar da wasu kananan ma'aikata kimanin 500.

Tun a watan Afrilun shekarar 2018, kamfanin PowerChina, ya fara kafa turakan lantarki tare da maye gurbin wadanda aka lalata a Juba, har ma an kusa kammala aikin, bayan da kamfanin a kwanakin nan ya fara kafa kanana da matsakaitan turakan lantarki da za su iya samar da wutar lantarki mai karfin megawatts 100.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China