Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD na hadin gwiwa da Sudan ta kudu wajen dakile cin zarafin al'umma ta hanyar lalata
2019-05-28 10:19:09        cri

Asusun kula da yawan al'umma na MDD ko UNFPA a takaice, na aiki da mahukuntan kasar Sudan ta Kudu, a fannin karfafa sashen shari'a, domin yaki da laifuka masu alaka da cin zarafin al'umma ta hanyar lalata.

Wakiliyar asusun na UNFPA a kasar Mary Otieno ta bayyana cewa, kasar dake gabashin Afirka, na bukatar cikakken tsari na kasa baki daya, wanda zai game sassan dokoki masu nasaba da wannan matsala, domin cimma burin da aka sanya gaba na kawo karshen matsalar.

Otieno ta kara da cewa, asusun da hadin gwiwar ma'aikatar kula da harkokin jinsi, yara kanana da walwalar al'umma, tare da ma'aikatar shari'a da harkokin kundin mulkin kasa, sun dukufa wajen samar da wani tsari na doka, wanda zai tunkari wannan kalubale a dukkanin sassan kasar.

Da yake tsokaci game da hakan, ministan shari'ar kasar Paulino Wanawilla Unango, ya jinjinawa gudummawar MDD a fannin yaki da laifuka masu nasaba da cin zarafin al'umma ta hanyar lalata, da sauran laifuka masu nasaba da keta martabar jinsin bil Adama, yana mai cewa, Sudan ta kudu da sauran kasashen duniya, na shan fama da wannan kalubale.

A nata tsokacin kuwa, ministar ma'aikatar kula da harkokin jinsi, yara kanana da walwalar al'umma Awut Deng Achuil, cewa ta yi hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar ta da fannin shari'a, na taimakawa wajen yaki da laifuka masu nasaba da cin zarafin al'umma ta hanyar lalata, inda ake fitar da karin dabaru, na toshe kafofin kubutar masu aikata laifuka dake da nasaba da hakan.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China