Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karfafa dangantaka da Sin zai bunkasa Sudan ta kudu
2019-10-27 15:41:46        cri

Masana sun bayyana cewa, karfafa dangantaka tsakanin Sudan ta kudu da kasar Sin yana da matukar alfanu ga ci gaban fannonin siyasa, tattalin arziki, da bunkasa kayayyakin more rayuwa a kasar ta gabashin Afrika.

Sudan ta kudu kasa mafi karancin shekaru a duniya, za ta koyi darrusa masu yawa daga salon ci gaban kasar Sin kamar bangarorin da suka shafi yaki da fatara, bunkasa tattalin arziki, da bunkasa zuba jarin kasashen waje, Liu Hongwu, daraktan cibiyar nazarin kasashen Afrika a jami'ar horas da malamai ta lardin Zhejiang na kasar Sin, ya bayyana hakan a lokacin dandalin tattaunawar kwararrun Sudan ta kudu da na kasar Sin karo na farko, wanda aka bude a ranar Juma'a a Juba.

Dandalin ya kunshi bangarori uku ne da suka hada da bangaren siyasa, sha'anin mulki da kuma tattalin arziki, taron ya tattaro malaman jami'o'i daga kasashen Sudan ta kudu da Sin, da masu nazarin al'amurra, da kwararrun masana, da kungiyoyin fararen hula, inda suke tattauna muhimman damammakin da kasashen biyu za su cimma na samun bunkasuwa.

Samson Wasara, daraktan cibiyar zaman lafiya, raya kasa, da tabbatar da tsaro a jami'ar Juba, ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Sudan ta kudu ta fara ne tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta daga kasar Sudan a watan Yulin shekarar 2011, a wasu muhimmman bangarori da suka hada da samar tallafin jin kan bil adama, da shirin wanzar da zaman lafiya sun taimaka wajen ceto rayukan al'ummar kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China