Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#CIIE#Sin za ta rungumi matakai 5 na inganta kara bude kofa
2019-11-05 10:45:36        cri

A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin kasarsa za ta rungumi matakai 5 na kara inganta bude kofa.

Matakan sun hada da ci gaba da fadada bude kofar kasuwanni, da ci gaba da kyautata tsare-tsaren manufar bude kofa, da ci gaba da inganta yanayin kasuwanci, da kara zurfafa dangantaka tsakaninta da kasa da kasa, da kuma ci gaba da hada hannu wajen ginin shawarar ziri daya da hanya daya.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar yau Talata a birnin Shanghai, yayin bikin bude taron baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China