![]() |
|
2019-11-05 10:33:45 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a gun taron bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu yau Talata a birnin Shanghai, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta hada kansu don kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa da hadin kai.
A cewarsa, ya kamata a nace ga bude kofa da samun bunkasuwa, da zurfafa mu'ammala, sannan kuma a yi adawa da manufar kariyar ciniki da ta bangaranci, da kuma sassauta shingen ciniki da ingiza bunkasuwa da kyautatuwar tsare-tsaren ciniki a duniya, ta yadda za a biya bukatun kasuwar duniya cikin hadin kai. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China