Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNDP zai fara wani shirin daidaita al'amura a yankin arewa mai nisa na Kamaru
2019-10-09 19:11:48        cri

Shirin raya kasashe na MDD (UNDP) ya sanar a Talatar nan cewa, zai fara wani shirin daidaita al'amura a yankuna 9 dake yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru da mayakan Boko Haram suka yiwa barna.

Wakilin shirin dake kasar Kamaru Jean Lu-Stalon shi ne ya sanar da hakan a Yaounde, babban birnin kasar, yana mai cewa, shirin na UNDP zai tura tawagogi zuwa wadannan yankuna 9 da za su amfana da shirin, domin tantance al'amura, ta yadda za a fara aiki ba tare da wani bata lokaci ba.

Minista a ma'aikatar tattalin arziki, tsare-tsare da raya yankuna na kasar Kamaru, Paul Tasong, ya bayyana cewa, shirin zai samar da doka, tsaro, kayayyakin more rayuwar jama'a, da ayyukan da suka shafi tattalin arziki da jin dadin jama'a a wadannan yankuna guda 9.

Za a gudanar da shirin ne na tsawon shekaru biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China