Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutane 100,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a yankin arewa mai nisa na Kamaru
2019-10-15 10:03:48        cri

Hukumomi a Kamaru, sun ce sama da mutane 100,000 da iyalansu, da ambaliyar ruwa ta raba da matsugunai, bayan kogin Lagone dake yankin arewa mai nisa na kasar ya yi ambaliya.

A cewar shugaban yankin Mayo-Danay, Oumara Maliki, ambaliyar ta auku ne da safiyar jiya Litinin, biyo bayan ruwan saman da aka yi ranar Lahadi, lamarin da ya shafi yankunan Mayo-Danay da Logone et Chari.

Ya ce har yanzu lamarin na tada hankali, domin mutane sun rasa komai na su. Inda ya ce har yanzu ba su kai ga gano barazanar da iftila'in ya yi ba.

Ya ce an samu masu fama da cutar amai da gudawa da zazzabin typhod da na malaria. Baya ga haka, akwai wadanda suka ji rauni saboda rushewar gini a kan su, yana mai cewa, suna kokarin ceton su.

A cewar hukumomin, masu aikin ceto na bincike domin gano wadanda suka bata, kuma ana fargabar tasirin ambaliyar kai ga ta'azzara karancin abinci da talauci da ake fama da su a yankin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China