Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru na sa ran samun lambobin yabo a gasar wasannin soji ta duniya
2019-10-15 09:55:10        cri

Yan wasan Kamaru sun baro kasar a jiya Litinin, domin halartar gasa karo na 7 ta wasannin soji ta duniya, wanda za a fara ranar 18 ga wata a birnin Wuhan na kasar Sin. Kafin tasowarsu zuwa kasar Sin, ministan tsaron kasar, Joseph Beti Assomo, ya bayyanawa 'yan wasan cewa, dole ne su shiga a dama da su a gasar, tare da cin nasara, har ma da samowa kasar lambobin yabo.

Yan wasan na Kamaru za su fafata ne a fannoni 6 da suka hada da kwallon kafa ta mata, da kokawa, da wasan taekwando, da guje guje da tsalle tsalle, da wasan judo, da kuma dambe.

A cewar Veronique Aboui, daraktar sashen kula da wasanni da al'adu na ma'aikatar tsaron kasar, wasannin gasar na da muhimmanci, musamman ga kungiyar kwallon kafa ta mata sojoji, saboda Kamaru za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta mata sojoji ta duniya da za a yi a badi. Don haka, ta ce wasannin na kasar Sin za su taimakawa kungiyar Kamaru kara zama cikin shiri.

Tun daga shekarar 1995 hukumar shirya wasannin sojoji ta duniya ke shirya gasar bayan duk shekaru 4. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China