Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun zafafa kai hare-hare kan kungiyoyi masu dauke da makamai
2019-11-04 09:14:05        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun kara zafafa kai hare-hare kan mayakan Boko Haram da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai dake addabar jama'a a sassan kasar.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin kasar dake yankin arewa maso gabashin Najeriyar Aminu Iliyasu ya rabawa manema labarai, rundunar ta ce, a baya-bayan nan ta yi nasarar kawar da wasu abubuwan fashewa da mayakan Boko Haram suka binne, musamman a jihohin Borno da Yobe dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Jami'in ya ce, dakarun sun kai samame kan sansanin mayakan na Boko Haram dake garin Kerenoa a karamar hukumar Marte na jihar Borno, inda 'yan ta'addan suka gudu daga sansanin bayan da suka hangi sojojin na zuwa.

Bugu da kari, sojojin sun kai irin wannan samame kan wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Birnin Gwari, yayin da suke gudanar da sintirin da suka saba a jihar Kaduna dake yankin arewa maso yammacin kasar dake fama da matsalar tsaro, inda suke farautar mambobin kungiyar.

A lokacin samamen da suka kaddamar a ranar 29 ga watan Oktoba, sojojin sun yi nasarar kubutar da mutane 7 da aka yi garkuwa da su, yayin da 'yan ta'addan suka bace cikin daji dake kusa suka bar mutanen da suke garkuwa da su.

A wani samamen da sojojin suka kaddamar a yankiin arewa masu yammacin kasar, nan ma sun yi nasarar kubutar da wasu mutane biyu da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a baya a karamar hukumar Isah dake jihar Sokoto.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China