Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NDLEA ta yi nasarar kama masu samarwa mayakan Boko Haram miyagun kwayoyi
2019-10-04 15:12:55        cri

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta tabbatar da cewa, dakarunta sun yi nasarar damke mutane 21 da ake zaton suna samarwa mayakan Boko Haram miyagun kwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar John Achema, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, an damke wadanda ake zargin ne a garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Achema ya ce, tuni 9 daga cikin su suka amsa laifin da suka aikata, kana an gurfanar da su a gaban wata kotu a Jalingo. Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincke kan ragowar.

A cewarsa, mutanen suna kokarin kaiwa mayakan Bokon Haram miyagun kwayoyin ne a sansanoninsu a lokacin da dakarun hukumar suka tare hanyar da suke amfani da ita wajen kaiwa 'yan ta'addan miyagun kwayoyin.

Ya ce, an yi nasarar gano kilogram 229.6 na miyagu da sauran haramtattun kwayoyi yayin samamen.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China