Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojan Najeriya ta ceto yara 25 da mayakan Boko Haram ke amfani da su a matsayin sojoji
2019-10-04 15:16:47        cri

Rundunar sojan Najeriya ta bayyana cewa, ta mikawa gwamnatin jihar Borno da asusun kula da kananan yara na MDD sama da yara 25 da ta kubutar daga hannun mayakan Boko Haram da take amfani da su a matsayin sojoji.

Kwamandan rundunar sojojin kasa na Najeriya dake yankin arewa maso gabashin kasar, Olusegun Adeniyi, ya bayyana cewa, an ceto yaran dake tsakanin shekaru 8 -16 ne yayin wani samame da dakarun rundunar suka kaddamar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake mika yaran ga gwamnatin jihar Borno da asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF) yayin wani bikin da ake shirya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ya bayyana cewa, sun mika yaran ne kamar yadda tsarin kasa da kasa ya tanada.

Ya ce, hakan ya nuna cewa, sojojin Najeriya sun himmatu wajen yaki da Boko Haram, da nufin kare wani rukunin al'umma da galibi wannan matsala ta fi shafa har ma ake tilasta musu shiga aikin soja.

Adeniyi, ya ce, shirin wani bangare ne na ceto yaran da aka tilasta musu shiga aikin soja. Galibin yaran da suka hada da maza 23 da mata 2, an ci zarafinsu, har ma ta hanyar yin lalata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China