Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin sojojin sama ya hallaka 'yan ta'adda masu yawa a arewa maso gabashin Najeriya
2019-10-06 15:29:42        cri

Wani jami'in sojojin Najeriya ya ce, harin da sojojin saman kasar suka kaddamar a maboyar mayakan 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram ya yi sanadiyyar hallaka mayakan masu yawa a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Harin wanda ya haddasa mummunar barna kan 'yan ta'addan a maboyarsu dake Kirta Wulgo a kusa da yankin tafkin Chadi, a cewar Ibikunle Daramola, kakakin rundunar sojojin saman kasar cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Daramola ya ce, dakarun sojojin saman musamman na rundunar sintiri ta Lafiya Dole ce ta kaddamar da harin a ranar Juma'a.

Sojojin saman sun kaddamar da hare haren ne bayan kammala wani binciken tattara bayanan sirri, inda suka gano mafakar da mayakan ke amfani da ita wajen shiryawa da kaddamar da hare haren ta'addanci.

Ya ce jiragen saman yakin sun gano takamammen maboyar 'yan ta'addan, inda daga bisani suka kaddamar da hare haren kansu suka lalata maboyar tare da hallaka 'yan ta'addan masu yawa. Daramola ya ce, rundunar sojojin saman Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da rusa dukkannin maboyar 'yan ta'addan dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China