Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da matakin Amurka na fakewa da batun Xinjiang wajen hana 'yan kasarta Visa da sanyawa kamfanoninta takunkumi
2019-10-09 19:37:54        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa tana adawa da matakin Amurka na fakewa da batun take hakkin bil-Adama a yankin Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa, tana sanyawa kamfanoninta takunkumi da ma hana wasu jami'anta takardun iznin shiga Amurkar.

.A ranar Litinin ne dai, ma'aikatar kasuwancin Amurka ta kara sanya wasu hukumomi da kamfanonin 28 na kasar Sin, cikin jerin sassan da za ta sanya musu takunkumi wai da sunan keta hakkin bil-Adama a yankin Xinjiang.

A jiya ne kuma, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce, kasarsa za ta hana wasu jami'an kasar Sin Visa, saboda wannan dalili. Sai dai Geng ya ce, matakin na Amurka ba shi da tushe, kana ya saba ka'idojin alakar kasa da kasa.

Ya ce, batun Xinjiang, batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, yana mai nanata cewa, kasar Sin ta dauki matakan kafa cibiyoyin koyon sana'o'i a yankin ne, domin yaki da ayyukan ta'addanci. Kuma babu batun take hakkin dan-Adam a yankin Xinjiang,(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China