Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ta rutsa da mutane 35,000 a arewa maso gabashin Nijeriya
2019-11-02 15:04:33        cri

MDD ta ce ambaliyar ruwa mafi muni da aka samu cikin shekaru 7 a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Nijeriya, ta rutsa da mutane 35,000, inda 19,000 daga cikinsu suka rasa matsugunansu.

Farhan Haq, mataimakin kakakin MDD ya bayyana a jiya cewa, gwamnatin Nijeriya ce ke jagorantar ayyukan agajin da samar da matsuguni ga mutanen da suke bukata, yayin da MDD da abokan huldarta ke taimakawa wajen samar da ruwa da kayayyakin tsafta da magunguna da sauran abubuwan bukata.

Jami'in ya ce, jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin dake fama da rikcin da ya shafe shekaru 10 ana yi a yankin arewa maso gabashin Nijeriya. Yana mai cewa, har yanzu akwai wasu mutane miliyan 7.1 dake bukatar agajin gaggawa.

Ya ce shirin ba da agajin jin kai ga Nijeriya na MDD a bana, na bukatar dala miliyan 848, domin taimakawa mutane milliyan 6.2, amma kaso 59 cikin dari na kudin kawai aka samu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China