Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kubutar da dalibai 4 da aka yi garkuwa da su a arewacin kasar
2019-10-16 09:11:48        cri

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar cewa, dakarunta sun yi nasarar ceto ragowar dalibai hudu wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna dake arewacin kasar.

Daliban suna daga cikin dalibai 10 na makarantar sakandaren gwamnati ta Gwagwada, dake garin Chikun a jihar Kaduna, wadanda aka yi awon gaba da su da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Dama dai tuni sojojin sun kubutar da dalibai 6 daga cikinsu bayan da suka bincika wani daji dake yankin tun a ranar da aka sace su.

Sauran ragowar daliban 4, an kubutar da su ne a ranar Litinin kuma tuni an sake sada su da iyalansu, a cewar Ezindu Idimah, kakakin rundunar sojojin jihar Kaduna.

Idimah ya ce, dukkanninsu babu wanda aka raunata, ya bayyana yadda dakarun sojojin suka samu nasarar aikin sintirin inda suka yi amfani da dabaru wajen gano maboyar 'yan bindigar.

Ya kara da cewa, 'yan bindigar sun tsere sun bar daliban 4 bayan musayar wuta da suka yi tsakaninsu da sojojin. Wasu mayakan sun tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga a jikinsu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China