Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare janar na MDD ya yi Allah wadai da harin ta'addaci a Najeriya
2019-06-18 09:48:47        cri

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da babbar murya game da tagwayen harin kunar bakin wake da aka kaddamar a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda kakakinsa ya bayyana.

Guterres ya bayyana ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su da gwamnatin Najeriya har ma da mutanen kasar baki daya. Kana ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka, in ji Stephane Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren.

Sakatare janar na MDD ya bukaci a binciko wadanda ke da hannu wajen shirya harin domin gurfanar da su a gaban shari'a.

Mista Guterres, ya jaddada goyon bayan MDD ga gwamnatin Najeriya a yakin da take yi da ayyukan ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi. Kana ya sake nanata cikakken goyon bayan MDDr wajen yaki da ayyukan ta'addanci a shiyyar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A kalla mutane 30 ne suka mutu, kana wasu mutanen 42 suka samu raunuka a harin kunar bakin waken da aka kaddamar da yammacin ranar Lahadi wanda ake zargin mayakan Boko Haram sun yi amfani da 'yan kunar bakin wake har guda uku suka daura ababen fashewa a jikinsu suka tada boma boman a wani filin kallon wasan kwallon kafa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China