Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bayani kan taro na 4 na kwamitin kolin JKS na 19
2019-11-01 19:09:20        cri

Jiya Alhamis aka kammala cikakken taro na 4 na kwamitin kolin JKS na 19, yau kuma ma'aikatar yada manufofin gwamnati ta kwamitin tsakiya na JKS ta kira taron manema labarai, inda aka bayyana cewa, yayin cikakken taron, an samu sakamako a bangarori biyu, wato a karo na farko za a fara yin nazari kan tsarin tafiyar da harkokin kasar, kana karo na farko da aka fitar da wani shirin da za a aiwatar da shi bisa matakai uku wato nan da shekarar 2021, cika shekaru 100 da kafa JKS, da shekarar 2035, da kuma shekarar 2049, cika shekaru 100 da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ana iya cewa, taron yana da babbar ma'ana a tarihin kasar ta Sin.

Mataimakin ministan ma'aikatar yada manufofin gwamnati ta kwamitin tsakiya na JKS kuma mataimakin darektan ofishin nazarin manufofin kasa na kwamitin tsakiya na JKS Wang Xiaohui ya bayyana cewa, sabbin matakan da kasar Sin za ta dauka sun fi mai da hankali kan yadda za a nace da kuma kyautata jagorancin JKS da tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, duk wadannan sun nuna cewa, kasar Sin tana aiwatar da manufofin da suka dace a kasar bisa doka.

Game da batun bullo da sabon tsarin tattalin arziki mai salon bude kofa a kasar, jami'an da abin ya shafa sun bayyana cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara kyautata tsarin a bangaren bude kofa, tare kuma da kara bude kasuwarta ga sauran kasashen duniya, ta yadda za a ingiza cinikayya maras shinge da saukaka harkokin zuba jari a kasar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China