Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sake bukatar wasu kasashe da su daina tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe
2019-10-30 20:22:55        cri

Jiya Talata, yayin taron tattaunawar da kwamiti na uku na babban taron MDD na 74 da kwamitin yaki da kabilanci na MDD suka kira cikin hadin gwiwa, wasu kasashen yamma kamar Amurka da Birtaniya sun zargi matakan da kasar Sin ta dauka a jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar.

Kan wannan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya mayar da martani cewa, kasar Sin tana son wadannan kasashe su daina tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe ta hanyar fakewa da batun kiyaye hakkin dan Adam, haka kuma su daina hada batun kiyaye hakkin dan Adam da manufar siyasa, haka kuma su daina yin amfani da ma'auni iri biyu kan batun.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yau, Geng Shuang ya bayyana cewa, yayin taron tattaunawar MDD da aka kira jiya, wakilan kasashe sama da 60 sun nuna goyon baya ga matsayin kasar Sin kan batun Xinjiang, kuma sun jinjinawa ci gaban da kasar Sin ta samu a bangaren kiyaye hakkin dan Adam da manufofin da kasar Sin take aiwatarwa domin tafiyar da harkokin jihar Xinjiang, har sun nuna adawa da yadda wasu kasashe suke neman tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun kiyaye dan Adam, duk wadannan sun nuna cewa, zai yi matukar wahala zargin da ake yi wa kasar Sin ba gaira ba dalili ya samu amincewa daga wajen al'ummun kasashen dunjya, ko shakka babu ba za su cimma makarkashiyarsu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China