Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta taya jam'iyyar ANC ta Afirka ta kudu murnar lashe zabe
2019-05-13 20:11:53        cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, Afirka ta kudu babbar kasa ce wadda take da babban tasiri a harkokin shiyya shiyya da ma harkokin kasa da kasa, a don haka babban zaben da aka yi a kasar ya jawo hankalin jama'a matuka, yanzu haka an kammala babban zaben cikin kwanciyar hankali kuma jam'iyyar ANC ta lashe kujeru masu rinjaye. Kasar Sin ta taya ta murnar nasarar da ta samu.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan alakar dake tsakaninta da Afirka ta kudu, tana kuma fatan za ta yi hada kai da sabuwar gwamnatin kasar dake karkashin jagorancin jam'iyyar ANC domin kara karfafa fahimtar juna a bangaren siyasa da hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu, ta yadda za su ciyar da alakar sada zumunta daga duk fannoni bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu gaba lami lafiya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China