Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin koli na JKS na 19 ya kammala zamansa na hudu
2019-10-31 19:41:03        cri

A yau Alhamis ne, kwamitin koli na JKS na 19 ya kammala cikakken zamansa na 4 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, tare da fitar da sanarwar bayan taro.

Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya gabatar da muhimmin jawabi yayin zaman da ya gudana karkashin jagorancin hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS.

A cewar sanarwar bayan taron, yayin zaman an saurara tare da tattauna rahoton aiki da Xi ya gabatar, wanda aka damkawa hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS. Bugu da kari, yayin zaman an yi bita tare da amincewa da shawarar da kwamitin koli na JKS ya amince da ita kan wasu manyan batutuwa da suka shafi yadda za a gudanar da inganta tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin da kara zamanantar da tsarin kasar da karfin tafiyar da harkokin mulki, kamar yadda Xi ya yi bayanin daftarin ga zaman kwamitin.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa, tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, tsari ne na kimiyya da jam'iyya da al'umma suka tsara ta hanyar dogon lokacin da suka dauka suna gwada shi

Sanarwar ta kara da cewa, tsarin shugabancin kasar Sin yana gudanar da duk wani aiki da wasu abubuwa ne kamar yadda tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin ya tanada. Sannan tsarin kasar da karfin jagorancinta, alamu ne na tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin da yadda take aiwatar da doka. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China