Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon musamman na Afirka ta kudu ya nemi afuwa bisa hare-haren kyamar baki ga 'yan Najeriya
2019-09-17 19:26:55        cri

Yau Talata kafofin watsa labarai na gwamnatin kasar Afirka ta kudu, sun gabatar da rahotanni dake nuna cewa, yanzu haka huldar diplomasiya dake tsakanin Afirka ta kudu da Najeriya ta gamu da matsala, saboda hare-haren kin jinin bakin da suka auku a kwanakin baya, a don haka shugaban kasar Afirka ta kudu ya aike da manzon musamman Jeff Radebe zuwa ga Najeriya.

A yayin ganawar sa da manzon musamman na shugaban tarayyar Najeriya Muhamadu Buhari a jiya, ya mika sakon neman afuwar shugaban Afirka ta kudu ga shugaba Buhari, inda ya yi alkawari cewa, 'yan sandan Afirka ta kudu za su yi kokari matuka, wajen gurfanar da masu aikata laifuffuka a gaban kuliya.

Bayan tattaunawar su, shugaba Buhari ya bayar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, ya riga ya yarda da sakon neman afuwar takwaransa na Afirka ta kudu, kana ya yi alkawari cewa, zai yi kokari domin inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Alkawuran da sassan biyu suka yi sun sassauta tsamin huldar dake tsakanin sassan, sun kuma share fagen ziyarar da shugaba Buhari zai kai a Afirka ta kudu a wata mai zuwa. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China