Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da matakin Amurka na fakewa da batun Xinjiang tana sanyawa kamfanoninta takunkumi
2019-10-08 19:16:27        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa tana adawa da ma Allah wadai da babbar murya, kan matakin Amurka ta sanyawa wasu bangarorin kasar 28 takunkumi wai da sunan keta hakkin bin Adam a yankin Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa dake yankin arewa maso yammacin kasar.

Mr Geng ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin da yake mayar da martani kan yadda Amurka ta kara fadada takaddamar cinikayyar da take da kasar Sin kan wasu manyan kamfanonin kwaikwayon tunanin dan-Adam na kasar Sin.

A don haka, kasar Sin tana kira ga bangaren Amurka, da ya hanzarta gyara kuskuren matsayin da ya dauka game da "halattattun matakan kasar Sin kan yaki da ayyukan ta'addanci".

Ya ce, kasar Amurka tana amfani da wasu zargi marasa tushe, don ta dakushe kanfanonin kasar Sin, kuma wannan mataki tamkar keta ka'idojin alakar kasa da kasa ne, sannan tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin.

Geng ya nanata cewa, Sin ta dauki matakai, da suka hada da kafa cibiyoyin koyon sana'o'i ne, da nufin yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini, kuma wadannan matakai sun samu yabo da goyon bayan al'ummomin kasa da kasa.

Jami'in na kasar Sin ya ce, kasarsa za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace, don tabbatar da tsaron kasa da muradunta. Don haka, ya bukaci Amurka, da ta janye wannan shawara ta kuma daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China